Yayin taron na yini 2, ana sa ran shugabannin kasashen za su yi nazarain kudurin kara karfafa hukumar AU, ta yadda za ta kara inganci, wanda shi ne jigon sauyin.
Shugaban Tarayyar kuma shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya ce manufar ita ce, karawa nahiyar karfi tare da samarwa al'ummarta makomar da ta dace da su.
Masu jawabi yayin bude taron, sun jadadda cewa sauyin ya zo a kan gaba, a lokacin da Afrika ke fuskantar kalubale saboda abubuwan dake faruwa a ciki da wajen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)