A wata sanarwar da hukumar ta AU ta fitar, ta musanta rahotannin, inda ta ce karya ce kawai aka kitsa da nufin kawar da hankulan jama'a daga ayyukan da dakarun tsaron suke yi a kokarinsu na murkushe mayakan al-Shabab, wanda dakarun na AU tare da jami'an tsaron kasar Somaliya ke gudanarwa bisa hadin gwiwa.
A ranar Litinin ne kungiyar 'yan ta'addan ta yi ikirarin hallaka sojojin kasar Habasha 30, wadnda ke aiki karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika wanda ta ce ta hallaka su a wani harin bam a yankin Hiraan.
Wasu boma bomai da aka dana a gefen hanya da ake sarrafa su da na'ura ne suka tashi da wasu tawagar jami'an tsaron a lokacin da suke kan hanyarsu daga BeletWeyne zuwa Kalabeyr a kusa da kan iyakar Somaliya da Habasha. Al-Shabab ta ce, abubuwan fashewa sun lalata motocin jami'an tsaron, inda kuma suka hallaka sojojin nan take.
Sai dai kuma, AMISOM ta ce sojojinta 4 ne kawai suka samu kananan raunuka, kuma ana ba su kulawa a wani asibiti dake kusa da yankin Beletweyene. (Ahmad Fagam)