in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta kaddamar da asusun wanzar da tsaro da zaman lafiya
2018-11-18 15:09:01 cri

Tarayyar Afrika AU, ta kaddamar da wani asusu a jiya Asabar, wanda ke da nufin inganta tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, Shugaban Rwanda, kuma shugaban Tarayyar mai ci, Paul Kagame, ya ce asusun zai yi aiki ne wajen tabbatar da magance kalubalen zaman lafiya da tsaro bisa matakan nahiyar.

Paul Kagame ya yi wannan jawabi ne a gefen taron shugabannin kasashe mambobin Tarayyar karo na 11 dake gudana a birnin Addis Ababa na Habasha, daga jiya 17 zuwa yau 18 ga wata.

Ya kuma ce asusun zai fara aiki ne da kudin da ya kai kusan dala miliyan 100 a ko wace shekara, inda shugabannin kasashe mambobin Tarayyar kawo yanzu suka bada dala miliyan 60.

Paul Kagame, ya yabawa kasashe 42 da suka bada gudunmuwarsu ga asusun, yana mai bukatar sauran kasashe mambobi 12 da su cike gibin.

Tarayyar Afrika na fatan amfani da asusun wajen kaucewa barkewar rikici da tabbatar da zaman lafiya da kuma batutuwan da suka shafi sake gina wuraren da suka yi fama da rikici. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China