"Ci gaban matasa muhimmin jigo ne a Afrika wanda za'a iya amfani da shi wajen cimma nasarori, da samar da makoma mai kyau da tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afrika, hakan zai samu ne ta hanyar amfani da 'yan kasashen domin a samu kyakkyawan wakilci da sauye-sauyen ci gaba a nahiyar har ma a matakin kasa da kasa,"in ji Ouedraogo.
"Lokaci ya yi da za'a yi kyakkyawan amfani da matasan Afrika a matsayin abokan hulda, a matsayin jari, kana a matsayin wani makami da za'a yi amfani da shi wajen yakar rashawa domin samun dawwamamman ci gaban nahiyar Afrika a halin yanzu," in ji jami'in.
Ya ce kungiyar tarayyar Afrika da mambobin kasashen suna bukatar yin hadin gwiwa, wajen zuba jari, da gina hanyoyin samun arziki, da samun kyakkyawar makoma, ta yadda matasan kasashen za su iya wakiltar nahiyar ta bangarorin fasaha, da kirkire kirkire da kuma fadada hanyoyin ci gaban samun arziki ga nahiyar.
Ouedraogo ya yi wannan kira ne a lokacin wani taron tattaunawa da kwamitin kwararru na matasa, da raya al'adu da kuma harkokin wasanni. (Ahmad Fagam)