in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan Afrika sun karbi horo kan aikin gona a Guizhou
2018-07-09 10:18:36 cri
Jimilar mutane 21 daga kasashen Afrika 6 ne suke karbar horo kan fasahohin aikin gona a Jami'ar Guizhou na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Mutanen da suka fito daga Habasha da Ghana da Mozambique da Nijeriya da Tanzania, na karbar horon ne karkashin wani shiri da aka fara a ranar 2 ga watan nan, wanda ake gudanarwa a Jami'ar Guizhou karkashin jagorancin ma'aikatar ilimi ta kasar Sin, inda zai shafe kwanaki 8 ana yi. Karkashin shirin, ana gudanar da taruka daban-daban da tafiye-tafiyen da suka kunshi fannoni da dama.

An kuma nunawa musu karbar horon yankunan raya kimiyya da aikin gona na kasar Sin, da yadda ake samar da mai da kayayyakin abinci da fasahar noman kayan lambu da lemar kwadi ba tare da gurbata muhalli ba da kuma fasahohin yaki da kwari.

Daya daga cikin masu karbar horon Karima I Babangida, wadda Darakta ce a Ma'aikatar aikin gona ta Nijeriya, ta ce tana fatan za su kai ilimi da fasahohin da suka koya daga kasar Sin zuwa Afrika, domin al'ummar nahiyar su amfana. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China