in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga kasashen duniya su yi kokarin kiyaye halittun daji
2017-03-04 13:49:21 cri
Shugaban babban zauren MDD Peter Thomsen da mataimakiyar babban sakataren majalisar Amina Mohammed a jiya Jumma'a, sun gabatar da jawabai dangane da ranar kiyaye halittun daji, inda suka yi kira da a dauki matakai a fannonin da suka hada inganta kafa dokoki da aiwatar da su da kuma hadin gwiwa don kiyaye halittun daji.

Babban zauren MDD, ya gudanar da muhawara ta musamman a wannan rana, inda Mr. Thomsen ya bayyana cewa, an kashe galibin kudaden da aka samu daga halastaccen cinikin halittun daji a kan rikicin 'yan tawaye da ayyukan ta'addanci, lamarin da ke haifar da barazana mai tsanani ga samun dauwamammen ci gaba, yana mai cewa, tilas ne a dauki manufa ta bai daya a duniya domin tinkarar matsalar.

A nata jawabi, Amina Mohammed ta ce, dole ne a dauki matakai da za su shafi bangarori biyu na masu sayar da halittun daji da kuma wadanda ke sayensu. Tana mai bada misali da samar da guraben aiki ga wadanda ke rayuwa a kusa da halittun daji ta yadda za su kiyaye su, da kuma, wayarwa masu sayen halittun kai game da illolin yin hakan.

Shi ma, wakilin kasar Sin na dindindin a MDD Liu Jieyi ya gabatar da jawabi, inda ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su kara kaimi wajen aiwatar da dokokin kariya da na yaki da cinikin halittun ta haramtaciyyar hanya.

Mr.Liu ya kara da cewa, tun daga shekarar 2015, kasar Sin ta fara yaki da cinikin hauren giwa, kuma nan da karshen shekarar 2017, za ta dakatar da sarrafa hauren giwa ba bisa ka'ida ba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China