in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun karuwar raya dazuka a Afrika duk da barazanar sauyin yanayi
2018-06-08 11:02:15 cri

Ana samun karuwar raya dazuka a Afrika cikin sauri sakamakon namijin kokarin da manoman nahiyar ke yi wajen dasa bishiyoyi, wani masanin dazuka ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis.

Godwin Kowero, babban sakataren dandalin gandun daji na Afrika (AFF), ya bayyana cewa, duk da karancin albarkatun dazuka gami da matsalar sauyin yanayi da ake samu, manoma suna da dabi'ar dasa bishiyoyi a gonakinsu, wanda hakan yana taimakawa wajen farfado da yawan bishiyoyi a nahiyar.

Kowero ya fada a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, aiwatar da tsarin dashen bishiyoyin babban cigaba ne wajen kara adadin bishiyoyi a sassan dazukan na Afrika.

Ya ce tsarin dashen bishiyoyin yana samun tagomashi a kasashen gabashin Afrika, musamman wuraren da ake da cunkoson jama'a, mutane suna dasa bishiyoyin a cikin gonakinsu da suke nomawa.

Kowero ya ce, daga shekarar 1990 zuwa 2012, manoman Jamhuriyar Nijar sun dasa bishiyoyi a kimanin filaye hekta miliyan 5 a cikin gonakinsu wanda ya taimaka matuka wajen raya gonakin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China