A jawabin da ya gabatar a taron hadin gwiwar majalisun dokokin kasar Habasha a ranar Litinin, shugaban kasar Habashan Mulatu Teshome, ya sanar cewa, kasarsa zata bullo da sabon tsarin bada biza ga dukkan mutanen dake dauke da takardun fasfo na kasashen Afrika da suke muradin shiga kasar, kana matakin zai fara aiki ne tun a shekarar 2018/19.
Da yake yin maraba da matakin da Habashan ta dauka, shugaban gudanarwar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yabawa dukkan kasashen mambobin kungiyar AU wadanda suka riga suka dauki matakan saukaka tsarin tafiye tafiye a tsakanin 'yan kasashen nahiyar ta Afrika.
Faki, ya bukaci dukkan kasashen mambobin kungiyar wadanda har yanzu basu aiwatar da wannan tsari ba dasu hanzarta daukar wannan mataki, kamar yadda wata sanarwa da AU ta fitar a ranar Laraba ta tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam)