Harriett Baldwin, ta ce maimakon maida hankali ga wani wa'adi na aikin tawagar, ya fi dacewa a maida hankali ga yanayin da kasar ke ciki, sa'an nan a janye dakarun sannu a hankali, gwargwadon karfin ikon tafiyar da tsaron kasar, da sojoji da sauran jami'an tsaron kasar ke da shi.
Wata sanarwa da tawagar AMISOM ta fitar a ranar Lahadi, ta rawaito Baldwin na cewa, har kullum Birtaniya na jaddada muhimmancin janye tawagar AMISOM bisa ikon dakarun soji da 'yan sandan kasar Somaliyar na kare kasar. Ta ce hakan shi ne mafi muhimmanci, ba wai wani wa'adi da aka tsara kan wani jadawali ba.
Ministar wadda ta ziyarci birnin Mogadishu a ranar Asabar, ta yabawa dakarun wanzar da zaman lafiya dake aiki karkashin tawagar AMISOM, ta na mai cewa kasar ta za ta ci gaba da nemawa tawagar cikakken goyon bayan kasashen duniya, a fannin samar da kudaden gudanar da ayyukan ta. (Fa'iza Mustafa)