in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sake farfadowar harkokin diflomasiyya tsakanin kasashen yankin kahon Afrika na haifar da kyakkyawar fata
2018-11-16 15:04:51 cri

Yayin da kasashen duniya ke dada amincewa da sauyin da yankin kahon Afrika ke samu na farfadowar yanayin diflomasiyya, su ma kasashen yankin da a baya ke fuskantar rikice-rikice, na kara kyautata fatansu game da samun ci gaban yanayin.

Bayan Kwamitin sulhu na MDD ya dage wasu takunkuman da ya kakabawa Eritrea, ciki har da na makamai a ranar Laraba, al'ummomin kasa da kasa sun bayyana kyakkyawan fata da kudurin taimakawa sauyin da ake samu a yankin kahon Afrika.

Shugaban hukumar Tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat, ya yi maraba da dage takunkuman, yana mai kira ga kasashen nahiyar da ma na duniya baki daya, da su taimakawa kasashen yankin wadanda al'amuransu ke daidaituwa a yanzu.

Faki Mahamat, ya karfafawa shugabannin yankin gwiwar tabbatar da dorewar yanayin da suke ciki, ta hanyar daukar dukkan matakan da ake bukata na zurfafa alaka da hadin gwiwa, yana mai jaddada cewar farfadowar dangantakar diflomasiyya manufa ce ta bai daya, ta wanzar da zaman lafiya da samun ci gaban nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China