in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamishiniyar AU ta yi kira da a kara azama wajen bunkasa kimiyya da kirkire kirkire a Afirka
2018-11-05 09:35:32 cri

Kwamishiniyar AU mai lura da sashen bunkasa kwarewar ayyuka, kimiyya da fasaha Sarah Anyang Agbor, ta yi kira ga daukacin sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen bunkasa harkokin kimiyya da kirkire kirkire a Afirka domin ciyar da nahiyar gaba.

Agbor ta yi kiran ne a ranar Lahadi, yayin taron musamman na shugabannin kasashen nahiyar 10, don bunkasa harkokin ilimi, kimiyya da fasasha na nahiyar. Taken taron dai shi ne "Bunkasa Ilimi, kimiyya da fasaha da kirkire kirkire a nahiyar Afirka".

Wata sanarwar da ofishin kungiyar hadin kan Afirka ta AU ya fitar game da taron, ta rawaito uwargida Agbor na jaddada kira ga kasashen nahiyar da su ninka kokarin su wajen bunkasa harkokin ilimi, kimiyya da fasaha a nahiyar, musamman ma fannin tabbatar da cimma sakamako mai gamsarwa, da tabbatar da aiwatar da ayyuka yadda ya kamata, da daukar matakan cimma nasarar hakan ba tare da wani jan kafa ba.

Har wa yau kwamishiniyar ta bayyana bukatar amfani da dukkanin damammaki da nahiyar ke da su, a wani mataki na fadada zuba jari ta hanyar shigar da karin albarkatun Afirka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China