in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci al'ummomin kasa da kasa su taimakawa rundunar kawance ta kasashen yankin Sahel
2018-11-16 11:06:44 cri

Wakilin kasar Sin a MDD, ya bukaci kasashen duniya su taimakawa rundunar kawance ta kasashe 5 na yankin Sahel, wadda aka kafa watanni 16 da suka gabata, da nufin magance kalubalen tsaro a yankin.

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu ne ya bukaci hakan a jiya, yayin zaman kwamitin sulhu na MDD kan kasashen yankin Sahel 5, inda ya ce dakarun rundunar na fuskantar kalubalen da suka hada da tabarbarewar tsaro a yankin da rashin kwarewa da na kayayyakin aikin da horo da kuma karancin kudi.

A watan Yulin 2017 ne kasashen 5 na yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso da Mali da Niger da Chadi da kuma Mauritania, suka kafa rundunar kawance da nufin yaki da ta'addanci da rashin tsaro, bayan rikicin 'yan a-ware na Tuareg da ya barke a arewacin Mali cikin shekarar 2012.

Sai dai, biyo bayan karancin kudi, rundunar kawancen ta gamu da matsaloli wajen cimma burinta.

Cikin wata sanarwa, Ma Zhaoxu, ya bayyana rundunar a matsayin gagarumar gudunmuwa ga zaman lafiya da tsaro a Afrika da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar samar mata taimako daga kasa da kasa.

Da farko, Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan ayyukan wanzar da tsaro, Jean-Pierre Lacroix, shi ma ya bayyana rashin isashen kudi a matsayin matsalar da rundunar ke fuskanta.

Ya ce kawo yanzu, ba a ware kusan kaso 50 na kudin da aka alkawartawa rundunar ba, bare ma a bayar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China