Rahoton jan jari na Afrika da Ernst & Young, da kamfanin tuntuba kan harkokin hada-hadar kudi ya hada, ya ce a bara, nahiyar Afrika ta samu ayyukan zuba jari 718, wanda ya karu da kaso 6 kan na bara waccan, bisa farfadowar tattalin arzikin nahiyar.
Rahoton, ya kuma bayyana kasashen da suka fi samun jarin, inda Habasha da Kenya da Zimbabwe suka samu gagrumin ci gaba a wannan fanni.
Afrika ta kudu da Morocco ne suka kasasnce matsayi guda na jagoran kasashen da suka fi samun jarin.
Rahoton ya kuma gano cewa, Afrika ta Kudu da Morocco da Kenya da Nijeriya da Habasha, su ne wadanda suka fi karfin tattalin arziki a yankunan da suke, wanda tattalin arzikinsu baki daya, ya mamaye kaso 40 na nahiyar. (Fa'iza Mustapha)