in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Ghana ya bukaci kara kwazo wajen yaki da laifuka ta yanar gizo
2018-10-02 16:40:10 cri
Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya bukaci daukar matakan da suka wajaba, wajen yaki da laifuka da ake aikatawa ta yanar gizo.

Mahamudu Bawumia ya yi kiran ne a jiya Litinin, yayin bikin kaddamar da shirin wayar da kai, game da tsaron yanar gizo na kasar na shekarar 2018.

Shirin da za a shafe wata guda ana aiwatarwa, zai mai da hankali ga wayar da kan 'yan kasar, game da illolin dake tattare da wannan matsala, da alfanun baiwa yanar gizo kariyar da ta dace a daukacin sassan kasar.

Kaza lika zai taimaka wajen yayata manufar gwamnati, ta tabbatar da tsaron yanar gizo, domin cimma nasarar harkokin kasuwanci da zamantakewar 'yan kasar.

Da yake tsokaci game da rahotanni daban daban, da suka nuna karuwar wannan matsala, Mr. Bawumia ya nuna damuwa bisa yadda hakan ke barazana ga tattalin arzikin duniya, da illa ga cin gajiya daga na'urori masu kwakwalwa, yana mai cewa gwamnati za ta yi tsayin daka, wajen tabbatar da ganin an shawo kan wannan kalubale a kasar.

Ya ce duniya na dada dunkulewa wuri guda ta fuskar amfani da na'urorin zamani, don haka yana da muhimmancin gaske, ko wace kasa ta maida hankali ga tsaron yanar gizo. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China