in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Duk da ana samun ci gaba ta fuskar karfawa mata a Afrika, har yanzu ana musguna musu
2018-10-06 15:16:12 cri
Wakilin kungiyar IPPF mai rajin tabbatar da tsarin iyali ta duniya a Afrika, Sam Ntelamo, ya ce kokarin da kasashen Afrika ke yi na karfafawa mata na samun dimbin nasarori a nahiyar.

Sam Ntelamo, wanda kuma shi ne wakilin hukumar kula da tattalin arziki ta MDD a Afrika, ya lura cewa, karin mata da dama na kasashen Afrika na shiga ana damawa da su a fagen siyasa, yayin da wasu ke samun ci gaba a fannin neman ilimi, ba kamar gomman shekarun da suka gabata ba.

Ya ce ya lura cewa, cikin lokaci mai tsawo da ya shude, matan Afrika da dama ba sa shiga siyasa kuma babu adadi mai yawa na 'yan mata a makaranta.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a farkon wannan makon, ya ce yanzu ba kamar baya ba, an samu gagarumin ci gaba, idan aka duba wasu kasashen dake da kaso 50 na mata a majalisun dokoki, wanda ya ce alama ce mai kyau.

Ya kuma yabawa nahiyar bisa karin adadin masu shiga makaranta da aka samu a kasashe da dama, baya ga karin 'yan mata dake zuwa makaranta har ma suke kammala karatun Firamare da Sakandare da kuma gaba da sakandare.

Jami'in ya kuma bukaci kasashen Afrika su yi aiki tukuru don kawo karshen yawan musgunawa mata a nahiyar da kuma ilmantar da yara maza da mata kan batutuwan da suka shafi tsarin iyali da kare samun juna biyu ba tare da aure ba da kuma cutukkan da ake samu daga jima'i. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China