Mohamed Ibn Chambas, ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa kwamitin sulhu na majalisar bayani game da ayyukan ofishin MDD a yammacin Afrika da yankin Sahel, da kuma abubuwan dake wakana a yanzu.
Da yake kira ga mambobin majalisar su taimakawa ayyukan jin kai da farfado da yankin, ya ce rikici tsakanin manoma da makiyaya na karuwa kuma babban barazanar tsaro ce da ka iya rikidewa zuwa hare-haren ta'addanci, wadda matsala ce da yankin ke fama da ita a yanzu.
A don haka, ya jadadda cewa, ya kamata duk wani matakin soji na tinkarar kalubalen tsaron ya kasance daidadi da aiwatar da wasu muhimman dabaru dake hada tsaro da agajin jin kai da ci gaba da kuma kare hakkokin bil adama.
Ya kara da cewa, wani batu kuma shi ne, karuwar fashin teku a mashigin Guinea, wanda ya hada da safarar miyagun kwayoyi da na kananan makamai da 'yan ta'adda ke yi, abun da ya bayyana a matsayin babbar barazana. (Fa'iza Mustapha)