in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da G5 Sahel sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa rundunar kiyaye tsaron shiyya
2018-03-25 13:26:54 cri

Babban jami'in shirin wanzar da tsaro da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika (AU), Smail Chergui, da babban sakataren kungiyar kasashe 5 na yankin Sahel wato G5 Sahel, Maman Sidiko, a ranar Jumma'a suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa rundunar tsaron hadin gwiwa don tabbatar da tsaron shiyyar kasashen biyar na yankin Sahel.

Bisa ga tsarin yarjejeniyar, kungiyar AU za ta tallafawa kasashen biyar na yankin Sahel wajen samar da karin kudade da za'a yi amfani da su ga ayyukan rundunar hadin gwiwar ta kasashen biyar na yankin Sahel, kamar yadda kungiyar ta AU ta sanar jiya Asabar.

Sanarwar ta ce wannan mataki ya kasance wani bangare ne na matsayar da majalisar AU ta cimma a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2017, inda ta amince da kafa dakarun tsaron hadin gwiwar yankin na Sahel.

Kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Nijar su ne suka kafa kungiyar ta G5 Sahel a shekarar 2014, a matsayin wani mataki na karfafa hadin gwiwarsu, da nufin tinkarar manyan kalubalokin dake addabar yankin.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar kasashen G5 Sahel ta jaddada aniyarta ta cigaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kungiyar AU.

Bayan da aka kulla yarjejeniyar, sakatariyar kungiyar ta G5 Sahel da rundunar dakarun za su cigaba da yin aikin hadin gwiwa da hukumar gudanarwar AU, da nufin cimma nasarar aiwatar da shirin tabbatar da zaman lafiya da tsaron shiyyar bisa hadin gwiwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China