in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Ya kamata a girmama rawar da nahiyar Afirka ke takawa kan yankin Sahel
2018-05-24 20:02:22 cri
Zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya ce, a yayin da ake fuskantar kalubalolin dake yankin Sahel, kamata ya yi kasashen duniya su girmama 'yancin kasashen nahiyar Afirka na taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalolinsu da kansu, kana su nuna goyon baya ga kasashe da kungiyoyin nahiyar wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin a yankin Sahel.

Wu ya bayyana haka ne a yayin taron bainar jama'a da kwamitin sulhu ya shirya game da batun rundunar sojojin hadin gwiwar kungiyar G5 na Sahel da aka shirya a jiya Laraba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China