in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata yankin Sahel ya zama kan gaba a kokarin MDD na wanzar da zaman lafiya
2018-06-30 16:23:04 cri
Tsoffi da sabbin Jami'an MDD, sun ce ya kamata yankin Sahel na Afrika ya ci gaba da zama kan gaba a kokarin Majalisar na wanzar da zaman lafiya.

Tsohon shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya na MDD Cho Tae-Yul wanda ya bayyana alakar hukumar da kwamitin sulhu na Majalisar, ya ce kwamitin ya bayyana muhimmancin rawar da yake takawa na shiga tsakani, tare da taimakon hukumar, da kuma mara baya ga yankin da hadin gwiwar ofishin MDD na yammacin Afrika da Sahel.

Jami'in ya ce abu ne mai muhimmanci a ci gaba da inganta shirin MDD na UNISS a yankin Sahel.

Ya ce yankin Sahel dake fuskantar kalubale da dama ciki har da sauyin yanayi da fari da ta'addanci da sauran wasu laifuffuka, ya tsawaita daga gabashin Senegal har zuwa yammacin Sudan, ya kuma yi kasa da yankin Sahara da ya hada da Mauritania da Mali da Burkina Faso da Niger da kuma Chadi.

Cho Tae-Yul, ya kuma bayyana wasu kasashen Afrika da hadin gwiwarsu da Kwamitin sulhu na MDD ya samar da kyakkyawan sakamako, yana mai bada misali da ci gaban zaman takewa da tattalin arzikin Burundi da kuma rawar da hukumar ta wanzar da zaman lafiya ta taka a Liberia, inda shirin wanzar da zaman lafiya na MDD ya shirya janyewa daga kasar a farkon bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China