in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a karfafawa mata a yankin Sahel
2018-07-11 11:06:40 cri
Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina Mohammed, ta yi kira da a yi kokarin bunkasa rawar da mata ke takawa a fannin tsaro da zaman lafiya a yankin Sahel.

Amina Mohammed wacce ba ta jima da dawowa daga taron shirin hadin gwiwa na MDD da Tarayyar Afrika game da kasashen yankin Sahel da suka hada da Sudan ta Kudu da Niger da Chadi ba, ta jadadda bukatar magance matsalolin da mata ke fuskanta yayin da ake rikici.

Ta shaidawa taron muhawara na kwamitin sulhu na MDD da aka yi kan mata da tsaro da zaman lafiya a yankin Sahel cewa, matsalolin abu ne da za a iya gani a Sudan ta Kudu. Ta ce sun ziyarci matan da suka nemi mafaka a sansanonin MDD, inda suka bayyana musu irin matsalolin da suka fuskanta a ciki da wajen sansanoni.

Ta kara da cewa, haka zancen yake ga matan yankunan karkara a Chadi, inda tasirin Boko Haram ya haifar da rashin tsaro da rashin 'yan uwa da kuma kara yawan amfani da mata a matsayin 'yan kunar bakin wake.

Amina Mohammed ta kuma jadadda bukatar sanya mata, da damawa da su da samar musu wakilci a dukkanin bangarori na rayuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China