in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son hada karfin kasa da kasa wajen bunkasa ciniki maras shinge, in ji firaministan kasar
2018-11-06 16:25:15 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da babbar darektar asusun IMF Christine Lagarde a jiya Litinin da yamma, inda ya ce, a yayin da ake fuskantar matsalolin rashin tabbas ga bunkasuwar tattalin arziki da kuma kariyar ciniki, kasar Sin na son kara hada gwiwa da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF da ma sauran hukumomin kudi na duniya, don inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki maras shinge tsakanin kasa da kasa.

Madam Christine Lagarde daga nata bangaren ta ce, IMF ya samu kwarin gwiwa sosai ganin yadda kasar Sin ke kokarin bude kofarta ga kasashen ketare, musamman ma burin da ta sanya a gaba da kuma fannonin da ta bude na kasuwar hada-hadar kudi, don haka yana son karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, don kiyaye bunkasuwar harkokin kudi da tattalin arziki mai dorewa a duniya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China