in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da Achim Steiner, shugaban hukumar kula da shirin neman ci gaba ta MDD
2018-11-02 10:43:45 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang,ya gana a jiya Alhamis da Achim Steiner, shugaban hukumar kula da shirin neman ci gaba ta MDD a nan Beijing, inda Li Keqiang ya bayyana cewa, hukumar, ita ce ta farko cikin hukumomin MDD da ta kulla hadin gwiwa da kasar Sin bayan da kasar ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje. Li Keqiang, ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwar a zo a gani da ta taimakawa kasar Sin sosai wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewarta.

Sannan ya nuna cewa, yanzu ra'ayoyin daukar matakai na kashin kai da kariyar cinikayya wadanda suke sanya duniya shiga hali maras kwanciyar hankali kuma maras tabbas, sun sake bullowa. Ya kara da cewa, a matsayin mambar dindindin ta kwamitin sulhu na MDD, kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin na sa ran kara yin hadin gwiwa da hukumomin MDD, ciki har da hukumar kula da shirin neman ci gaba, ta yadda za su iya kare manufofin daukar matakai daga bangarori da dama da odar duniyar da ake tabbatarwa bisa ka'idojin kundin tsarin mulki na MDD, domin shawo kan kalubalen da suke shafar duk duniya baki daya, sannan za a iya bunkasa karfin kasashe daban daban wajen neman ci gaba ba tare da tangarda ba bisa karfinsu, karkashin ka'idojin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa domin bayar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

A nasa bangaren, Mr. Achim Steiner ya bayyana cewa, hukumar kula da shirin neman ci gaba ta MDD tana da kyakkyawar huldar abota da kasar Sin, kuma bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa a fannoni daban daban a kasar Sin, har ma a fadin duniya. Ya ce hukumarsa ta yaba da kasar Sin da ta tsayawa ra'ayin daukar matakai daga bangarori da dama da rawar da MDD take takawa. Yana fatan kara yin hadin gwiwa da bangaren Sin a fannonin kirkire-kirkire da neman ci gaba ba tare da tangarda ba, har ma a fannonin ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma more fasahohin neman ci gaba da suka samu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China