Yayin zamansa a Singapore, Li Keqiang, zai halarci taron shugabannin kasashen kudu maso gabashin Asiya da Kasar Sin, karo na 21 da taron da Kungiyar za ta kuma yi da shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta arewa karo na 21, da kuma taro na 13 na kasashen gabashin Asiya.
Cikin tawagar Firaministan, har da Xioa Jie, Mamba, kuma Sakatare Janar na Majalisar gudanarwar kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)