Ministan ma'aikatar kiwon lafiya na tarayyar Najeriya Isaac Adewole, ya ce mahukuntan Najeriyar na daukar karin matakai, na rage matsalar mace macen mata masu juna biyu, tare da kawo karshen matsalar yaduwar cutar AIDs daga uwa zuwa jaririn ta nan da shekaru uku masu zuwa.
Ministan wanda ya bayyana wannan alwashi a birnin Abuja, yayin taron cika shekaru 10 da kafuwar kungiyar lura da yawan al'umma ta kasa da kasa ko PCI a takaice, ya kara da cewa gwamnati na fatan cimma nasarar kudurin ta, na ganin yara kanana sun kara samun zarafi na rayuwa cikin koshin lafiya nan da shekaru uku masu zuwa.
Mr. Adewole ya ce duk da cewa kasafin kudin kasar na bana, ba zai kai kasar inda take fata a fannin kiwon lafiya ba, amma duk da haka za a ga manyan sauye sauye, wadanda za su haska kyawawan manufofin gwamnatin mai ci.
Ministan ya kara da cewa, matakan da ake dauka za su baiwa al'ummar kasar damar samun karin kulawa ta bangaren lafiya, da ragewa 'yan kasar radadin matsin tattalin arziki, tare da samun managarcin tsarin kiwon lafiya. Har ila yau gwamnatin kasar na shirin samar da a kalla asibitocin sha ka tafi masu nagarta dai dai, a daukacin mazabun kasar, domin baiwa al'umma damar samun magani da kulawar likitoci.(Saminu Alhassan)