in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Ma'aikatan lafiya sun shiga yajin aiki
2018-04-18 20:34:49 cri

Gamayyar kungiyar ma'aikatan lafiya ta Tarayyar Najeriya ko NAHP a takaice, ta fara wani yajin aiki na sai baba ta gani a dukkanin sassan kasar, sakamakon zargin gwamnati da ta yi, na gaza cika alkawuran da ta dauka a baya.

Babban sakataren kungiyar Obisesan Oluwatuyi, ya bayyanawa 'yan jarida a birnin Abuja fadar mulkin kasar cewa, ba za su janye yajin aikin ba, har sai gwamnati ta biya masu dukkanin bukatun su.

Kafin hakan ita ma kungiyar gamayyar ma'aikatan lafiyar kasar ta JOHESU, ta sanar da fara gudanar da yajin aiki na duk kasa tun daga daren ranar Talata, tana mai cewa hakan ya biyo bayan kin cika alkawarun da gwamnatin kasar ta yi musu.

Jagoran kungiyar Josiah Biobelemoye, ya zayyana bukatun na su, wadanda suka hada da gyara tsarin biyan albashi na CONHESS, da wasu kudi da suke bin gwamnatin bashi karkashin tsarin albashi na CONHESS 10, da kuma bukatar kara daukar kwararrun ma'aikata a sashen lafiyar kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China