in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chana Za Ta Samar Da Hasken Lantarki Mega Watts 7,000 A Neja Delta
2018-07-04 09:51:04 cri
Mun samu wannan labari daga shafin Internet na "Leadership a Yau".

Hukumar kyautata yankin Neja Delta NDDC, ta shaida cewa, a yanzun haka tana kan tattaunawa da wani kamfanin kasar Chana, domin ya samar wa da yankin na Neja Delta hasken lantarkin da yake bukata.

Babban daraktan hukumar ne, Nsima Ekere, ya bayyana hakan, ta bakin daraktan hulda da jama'a na hukumar, Ibitoye Abosede, ranar Litinin a Fatakwal. Mista Ekere, wanda daraktan ayyukan hukumar, Samuel Adjogbe, ya wakilce shi ya fadi cewa, a tattaunawar da suka yi da wakilan kamfanin na kasar Chana mai suna, SINOTEC, cewa an tsara wannan aikin ne domin samar da ci gaban masana'antu a yankin. Ya bayyana cewa, da zaran an kammala aikin za a rarraba hasken lantarkin ne a sassa 18 da ke yankin.

Ya ce sun nemi wasu hanyoyin, amma sai muka tabbatar da ba zamu iya samun abin da muke bukata daga garesu ba, don ci gaban masana'antu a wannan yankin namu. Hakan ya sa ya zama tilas, an yi wani hobbasan wanda zai iya ba mu abin da muke nema, ta yadda za mu janyo hankulan masu zuba jari zuwa wannan yankin namu. Mista Ekere, ya ce, hukumar na su ta mayar da hankalinta ne kacokan wajen samarwa da yankin wata hanyar ta tattalin arziki, ba tare da dogaro da Man Fetur ko iskan Gas ba. A cewarsa, tuni suka kammala duba yanda za a gudanar da aikin a Jihohin na yankin Neja Delta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China