Da yake karin haske kwamandan bataliyar Guo Meng ya bayyana cewa, tawagar ta kunshi rukunin farko na sojojin wanzar da zaman lafiya 700 da kasar Sin ta tura. Aikin da za su gudanar sun hada da kare fararen hula da ma'aikatan MDD da amsu gudanar da ayyukan jin kai da yin sintiri, da yin rakiya da sauran ayyukan tsaro.
Dukkan mambobin bataliyar dai sun shafe watanni uku suna samun horo, kuma sun ci jarrabawar da aka shirya musu, lamarin da ya sa suka cancanci gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta kudu. (Ibrahim)