Laftana janar Xu wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka shirya don murnar cika shekaru 69 da kafa rundunar sojojin saman kasar Sin da ya gudana a birnin Zhuhai dake lardin Guangdong, ya ce kara gina rundunar sojojin sama ta zamani, ya dace da manufar gina tsaron kasa da ma dakarun kasar.
A cewarsa, matakin farko shi ne,nan da shekara ta 2020, za a gina rundunar da za ta kunshi harkokin zirga-zirga da karfi a fannin sararin samaniya da ma karfin kai hari da tsaro, ta yadda sabbin kayayyakin aikin da aka tanadar za su taimakawa wadanda ake da su a halin yanzu. Wannan wani mataki ne na kara karfin rundunar a dukkan fannoni.
Mataki na biyu, shi ne bukatar kara dabarun rundunar da ma zamanantar da manufofinta,da yiwa tsari da jami'ai da daukacin makamanta garambawul. Ana kuma fatan kammala gina rundunar da za ta dace da zamani nan shekarar 2035.
Mataki na uku a cewar jami'in shi ne, nan da tsakiyar karni na 21, ana fatan yiwa bakin dayan rundunar sojojin saman kasar ta Sin gyaran fuska ta yadda za ta kasance babu irinta a duniya baki daya.(Ibrahim)