Liu Chuanjian, da aka haifa a shekarar 1972, matukin jirgin sama ne a Sichuan, kuma ya yi fice ne saboda kwarewar da ya nuna, wajen saukar da jirgi, a lokacin da tagar gaban jirgin ta fashe yayin da jirgin ke sama, al'amarin da ya ceci rayuka 119 dake cikin jirgin
Sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na JKS da ma'aikatar kula da harkokin tsoffin sojoji ta kasar, sun ce sauran wadanda aka karrama sun hada da wadanda suka taka rawa wajen jagorantar fitar da kauyukansu daga talauci ko kuma kare rayuka da dukiyoyin al'umma, bayan sun bar aikin soja. (Fa'iza Mustapha)