in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar sojojin kasar Sin ta bukaci Amurka ta kasance mai nuna dattaku da sanin ya kamata
2018-09-28 09:59:34 cri
Ma'aikatar kula da al'amurran tsaro ta kasar Sin a jiya Alhamis ta sanar da cewa, Amurka ita ce ke da alhakin haifar da rashin jituwa game da alakar dake tsakanin sojojin Sin da na Amurka, don haka ta bukaci Amurkar ta kasance mai nuna dattaku da sanin ya kamata.

A taron da aka saba gudanarwa na manema labarai, Ren Guoqiang, kakakin ma'aikatar tsaron kasar, ya yi tsokaci a yayin da yake bada amsar tambayar da aka yi masa game da ikirarin da Amurka ta yi na sayarwa yankin Taiwan makamai, da batun kakabawa sojojin kasar Sin takunkumi, kana da ci gaba da tura dakarun tsaron Amurka yankunan tekun kudancin kasar Sin.

Ren ya jaddada aniyar kasar Sin na ci gaba da nuna adawa da wadannan manufofi, kana Sin ta bukaci bangaren Amurka da ta nuna sanin ya kamata da yin abin da ya dace wajen kyautata alakar dake tsakaninta da sojojin kasar Sin bisa nuna gaskiya, inda ta bukace ta da ta yi kokarin hadin gwiwar soji don daidaita alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Game da batun cinikin makamai, Ren ya ce, matsalar ba wai ta shafi adadin makaman ba ne, sai dai yadda za'a gudanar da tsarin.

Batun cinikin makaman zai yi matukar lalata dangantakar dake tsakanin sojojin Sin da Amurka, da kuma wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk yankin na Taiwan, in ji Ren.

Game da nuna tsokana kan batun tekun kudancin Sin kuwa, Ren ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace kan lamarin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China