in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar tsaron Sin ta shirya liyafar cika shekaru 91 da kafuwar rundumar PLA
2018-08-01 11:54:31 cri

Ma'ikatar tsaron Sin ta shirya bikin murnar cika shekaru 91 da kafuwar rundumar sojojin 'yantar da al'ummar kasar ta PLA, a ranar 1 ga watan Augustar nan.

Da yake jawabi albarkacin wannan rana, dan majalissar zartaswar kasar, kana ministan tsaron kasar janar Wei Fenghe, ya ce a madadin kwamitin tsakiya na JKS, da majalissar zartaswar kasar, da hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar ya mika sakon gaisuwa da jinjinawa ga daukacin sojojin kasar ta Sin, da dakarun 'yan sanda na rundunar, da sojojin ko ta kwana, da na musamman, da tsaffin sojoji da wadanda suka yi fice a aikin, da wadanda suka zamo abun misali.

Janar Wei Fenghe ya ce Sin za ta ci gaba da bin hanyar zaman lafiya domin wanzar da ci gaba, za ta dage kan bin hanyar kare kai, da aiki da sauran kasashe, wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

Janar ya kara da cewa, Sin za ta nacewa hanyar bunkasa sabon salon kawancen kasa da kasa, ta yadda za a kai ga gina al'umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama. Kaza lika za ta ba da gudummawa wajen wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, tare da daga matsayin dokokin kasa da kasa.

A daya bangaren kuma, Sin na kan bakanta, na wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya, tare da jaddada yankin Taiwan a matsayin bangare na Sin.

Ministan na tsaro ya ce ko shakka babu, rundunar PLA na da fatan nacewa kudurorin tabbatar da karfin gwiwar dakarunta, da aiwatar da manufofin yaki da masu rajin kawo baraka, "masu burin ware yankin Taiwan daga babban yankin kasar".

Rundunar za kuma ta dakile duk wani yunkuri na tsoma bakin wasu bangarorin waje cikin harkokin cikin gidan kasar. Daga karshe ya ce rundunar za ta tsaya tsayin daka wajen kare dalilan kafuwarta, za kuma ta yi aiki tukuru, wajen gina dakaru masu niyyar kare darajar al'umma, kuma masu matukar kwarewar aiki. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China