in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya yi tir da garkuwa da dalibai a arewa maso yammacin Kamaru
2018-11-07 10:34:40 cri
Babban magatakadar MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai, da garkuwar da aka yi da wasu malamai, da daliban makarantar sakandaren garin Bamenda dake arewa maso yammacin kasar Kamaru.

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta rawaito Mr. Guterres na kira da a saki wadannan bayin Allah, domin su samu damar komawa ga iyalansu ba tare da wani bata lokaci ba. Ya ce ba wani dalili na shari'a, da zai sanya a yi garkuwa da fararen hula, musamman ma yara 'yan makaranta.

Mr. Guterres ya jaddada bukatar amfani da yanayi na lumana, wajen warware tashe-tashen hankula da ke addabar yankunan arewa maso yamma, da kudu maso yammacin kasar ta Kamaru.

Yankunan biyu wadanda ke magana da Turancin Ingilishi dai sun dade suna zargin gwamnatin kasar da nuna masu wariya. To sai dai kuma MDD ta ce a shirye take ta ba da gudummawarta, domin kaiwa ga warware wannan takaddama. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China