in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya: An mayar da bakin haure 40,000 a kokarin da suke yi na shiga Turai a kowace shekara
2018-11-14 10:33:28 cri
Kasar Aljeriya ta sanar a jiya Talata cewa, a kowace shekara masu tsaron kan iyakarta na mayar da kimanin bakin haure 40,000 dake kokarin shiga Turai ta barauniyar hanya, a wani mataki na kokarin da kasar ke yi na hana kaurar jama'a ba bisa ka'ida ba.

Gidan rediyon Channel I ya ruwaito darekta mai kula da kaurar jama'a a ma'aikatar cikin gidan kasar Hassan Kacima na cewa, galibin mutanen dake kokarin shiga kasar ta kan iyakar kudancin kasar ta barauniyar hanya, sun fito ne daga kasashen Afirka 23 dake yammaci, da yankin Sahel da kuma yankunan Afirka ta tsakiya.

Ya kuma lura da cewa, kokarin bakin hauren shi ne isa gabobin Turai, don haka mahukuntan kasar ba za su kasa a gwiwa ba wajen dawo da su.

Ya ce, a wannan shekara kadai, mahukuntan kasar sun yi nasarar mika bakin haure kimanin 10,000 ga gwamnatin Nijar.

Jami'in ya ce, gwamnatin Aljeriya tana daukar batun tusa kyeyar bakin haure da muhimmancin gaske, wannan ne ma ya sa a shekarar 2018 da muke ciki gwamnatin kasar ta kebe dala miliyan biyar da nufin shawo kan wannan matsala. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China