"Bouteflika shi ne shugaban kasa kuma shugaban jam'iyyar. Ba mu da wani sauran dan takara a zaben shugaban kasar na shekarar 2019 sai Bouteflika," sakatare janar na jam'iyyar NLF mai mulkin Djamel Ould Abbas ne ya bayyana hakan.
Bouteflika, mai shekaru 81, yana fama da matsalolin rashin koshin lafiya bayan da ya kamu da cutar shanyewar jiki a shekarar 2013, tun daga wancan lokacin ya rage yawan fitowa a bainar jama'a.
An sake zabarsa a shekarar 2014 a wa'adin mulki karo na 4 wanda zai kare a shekarar 2019, Bouteflika wanda ake sa ran zai nemi wa'adin mulki a karo 5 matukar kundin tsarin mulkin kasar ya lamince masa, kamar yadda wasu masu sanya ido suka bayyana. (Ahmad Fagam)