Kasar Aljeriya, ta fitar da wani umarnin da ya shata wani yankin na musammam na teku da take da ikon amfani da shi, wanda ya yi hannun riga da gabar ruwan kasar.
Kamfanin dillancin labarai na APS ya ruwaito cewa, yankin wuri ne da kasar ke ikon amfani da shi ta fuskar hakar ma'adinai da amfani da albarkatun cikin ruwa.
APS ya ruwaito umarnin na bayyana cewa, an shata yankin ne daga dokar iyakance yanki ta watan Agustan 1984 bisa tsarin WGS shata yanki.
Yankin ya mika da nisan kilomita 370 daga gabar ruwan kasar. (Fa'iza Mustapha)