in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu sakamakon hadarin jirgin soji na Aljeriya ya kai mutum 257
2018-04-11 20:25:13 cri
Rahotanni daga kasar Aljeriya na cewa, yawan mutane da suka rasu sakamakon hadarin jirgin sojoji na kasar Aljeriya ya kai mutum 257.

Da sanyin safiyar Larabar nan ne dai wani jirgin na soji ya fadi a dab da sansanin sojoji na Boufarik, mai nisan kilomita 30 daga kudancin birnin Algiers.

Jirgin mai kirar Ilyushin I-76, na dauke ne da dakarun soji, ya kuma fadi a wani wuri maras mutane, dauke da sojoji sama da 250, a kan hanyar sa ta zuwa Bechar dake kudu maso yammacin kasar.

Tuni dai babban kwamandan askarawan sojin kasar, Laftana Janar Ahmed Gaid Salah, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su, tare da ba da umarnin fara bincike kan musabbabin aukuwar lamarin.

Sashen kashe gobara na kasar ya fidda wata sanarwa, wadda ke cewa an tura jami'an kashe gobara 300, da motocin daukar marasa lafiya 40, da wasu motocin na kashe wuta 40, domin gaggauta ceton wadanda wannan hadari ya rutsa da su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China