Ministan wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Algiers, babban birnin kasar, ya ce taron zai baiwa kasashen kungiyar ta OPEC damar hada kai don tattauna yadda za a daidaita farashin man a kasuwannin duniya.
Ya ce, farashin man ya tashi, saboda wasu dalilai na kasuwa, amma komai zai daidaita bayan an cimma daidaito kan yadda ake samar da man da kuma bukatarsa.
Ya kuma yi nuni da cewa, yarjejeniyar da aka cimma a watan Disamban shekarar 2016 tsakani kasashen kungiyar da wadanda ba sa cikin kungiyar, kamar kasar Rasha, kan yadda za a janye ganga miliyan 1.8 a kowa ce rana daga kasuwa, matakin ya taimaka wajen daga farashin man tsakanin dala 70 zuwa 80 kan kowace ganga.(Ibrahim)