Wata sanarwa da sojojin suka walklafa a shafinsu na Twitter,sun bayyana cewa, yarinyar mai suna Shaidatu Adamu 'yar shekaru 19 da haihuwa, an kama ta ne a lokacin da take kokarin shiga garin na Maiduuguri, sanye da rigar kunar bakin wake.
Ta kuma shaidawa jami'an dake binckenta cewa, ta shafe kusan shekaru uku tana samun horo a dajin Sambisa. Tuni dai aka tura kwararru a fannin abubuwan fashewa domin su kwance jigidar bama-bamai dake jikinta. An kuma fara gudanar da bincike don gano inda yarinya ta nufi kai harin.
Tun a shekarar 2009 ne dai kungiyar ta Boko Haram ke kokarin kafa shari'ar musulunci a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.
Kasashe hudu da rikicin na Boko Haram ya shafa sun hada da Chadi, Jamhuriyar Nijar da Najeriya, MDD na cewa, Boko Haram ta raba kusan mutane miliyan 2.4 da muhallansu a yankin tafkin Chadi. (Ibrahim)