in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun Najeriya ta hana belin shugaban 'yan Shi'a
2018-11-08 09:49:04 cri

Wata kotu dake zama a jihar Kaduna a arewacin Najeriya, ta hana bukatar neman belin shugaban kungiyar 'yan Shi'a ta Najeriya IMN Ibrahim El-Zakzaky da mai dakin sa Zeena. Rashin sakin su ne dai ya haifar da zanga-zangar baya bayan, da tashin hankali tsakanin magoya bayan malamin da 'yan sanda a birnin Abuja.

An dai gabatar da El-Zakzaky da mai dakin sa a karon farko gaban kotun, a ranar 15 ga wayan Mayun shekarar 2018, bayan damke su a garin Zaria dake jihar ta Kaduna a watan Disambar shekarar 2015.

Masu gabatar da kara sun zargi shugaban 'yan Shi'ar da wasu mutanen su 4, da hannu cikin aikata laifuka, da suka hada da shirya taro ba bisa ka'ida ba, da kisan kai, da kuntatawa al'umma, da tada hankulan al'umma da dai sauran su.

Mai shari'a Gideon Kurada, ya ce lauyoyin malamin, ba su gabatar da isassun shaidu na likita da za su sanya ya ba da belin malamin ba. Kurada ya ce malamin da mai dakin sa, za su ci gaba da kasance karkashin kulawar hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, har zuwa ranar 22 ga watan Janairun shekara mai zuwa, lokacin da zai sake sauraron bukatar ba da belin su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China