in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar cutar kwalara ta yi sanadin mutuwar mutane 175 a Nijeriya
2018-11-13 09:49:45 cri
Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway wato NRC, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar cutar kwalara a kalla jihohi 3 daga cikin 6 na arewa maso gabashin Nijeriya, ya karu zuwa 175 a farkon watan nan.

A karshen watan Satumba ne ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD da jami'ai a kasar, suka tabbatar da mutuwar mutane 97 sanadiyyar cutar.

Biyo bayan bincikenta na baya-bayan nan, NRC ta ce mutane 10,000 ne suka kamu da cutar a jihohin Adamawa da Borno da Yobe dake arewa maso gabashin kasar.

Birnin Maiduguri da ya kasance cibiyar kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, na dauke da 'yan gudun hijira 243,000 dake cunkushe a sansanoni, wadanda ke fama da karancin tsafta, al'amarin da ya bai wa cutar damar yaduwa.

Manajar shirin NRC a Maiduguri, Janet Cherono, ta ce yanayin cutar ta kara ta'azzara ne a lokacin damina. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China