in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta ware dala biliyan 1.3 don gudanar da wasu muhimman ayyuka 5
2018-11-07 10:53:50 cri
Gwamnatin Nijeriya ta ware dala biliyan 1.3 da za ta yi amfani da su wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka 5 a fadin kasar.

Ministan yada labarai da al'adu na kasar, Lai Mohammed, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce za a samo kudaden ayyukan ne daga asusun kula da ababen more rayuwa na fadar shugaban kasa wanda ke karkashin hukumar kula da dukiyar zuba jari ta kasar.

Ya ce da dala bilyan 1.3 na gudanar da aikin, asusun zai tabbatar da ayyukan 5 da a baya suka fuskanci matsala saboda karancin kudi, sun samu kudaden da ake bukata na aiwatarwa.

Ministan ya ce ayyukan sun hada da babbar titin Lagos zuwa Ibadan da titin Abuja zuwa Kano da wanda ya hada yankin gabashin kasar da yammaci da tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da kuma gadar Niger ta biyu.

Ya ce yanzu haka, tuni aka fitar da kudin fara aikin tashar wutar lantarki ta Mambila da na sauran ayyukan 4, kuma ya tabbata za a kammala su a daidai wa'adin da aka diba.

A cewarsa, zuwa yanzu, gwamnatin mai ci ta karbi rancen dala biliyan 10 domin aiwatar da ayyukan more rayuwa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China