in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Najeriya sun damke mutane 6 da ake zargi da hannu wajen kashe basaraken gargajiya
2018-11-08 09:38:37 cri
Jami'an 'yan sandan ciki a Najeriya sun sanar a jiya cewa sun cafke mutane 6 da ake zarginsu da hannu wajen kashe Maiwada Galadima, wani basaraken gargajiya a yankin arewacin jahar Kaduna.

Mutanen 6 sun hada da wasu da ake zarginsu mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram ne, an gabatar da su ga 'yan jaridu a babban birnin jahar.

Jami'an hukumar tsaron farin kaya na DSS ne suka damke mutanen a wurare daban daban, Mahmud Ningi, darakta hukumar DSS na jahar, shi ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da manyan jami'an tsaron jahar.

Galadima, wanda babban basarake ne a masarautar Adara wanda aka hallaka bayan an yi garkuwa da shi tare da matarsa a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan ziyarar da suka kai na duba irin hasarar rayuka da dukiyoyin da aka samu a lokacin wani tashin hankali da ya barke a yankin Kajuru dake jahar a watan jiya.

Sai dai matar ta tsira amma masu garkuwar sun kashe basaraken gargajiyar bayan sun karbi kudin fansa.

Wannan al'amari dai ya janyo wani sabon tashin hankali wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu yawa a jahar, lamarin da ya haddasa sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a birnin Kaduna da kewaye da nufin kawo karshen zub da jini a jahar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China