Sakataren zartaswa na kungiyar Mahboub Maalim ne ya bayyana haka, lokacin da yake ganawa ranar Lahadi, da Jakadan Kasar Sin a Djibouti Zhou Ruisheng.
Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce Mahboub Maalim, ya yabawa dangantakar dake kara habaka tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin IGAD, bisa moriyar juna da alakar kasa da kasa mai karfi.
Yayin ganawar, Mahboub Maalim, ya ce a shirye yake, ya kai ziyarar aiki ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin domin gabatar mata da manufofin kungiyar.
A wani bangare na ganawar, gwamnatin kasar Sin, ta hannu jakadan nata na Djibouti, ta mika tallafin kudi dala 100,000 ga kungiyar IGAD. (Fa'iza Mustapha)