Sakataren zartaswa na kungiyar IGAD Mahboub Maalim, wanda ya ce raya ababen more rayuwa jigo ne ga samar da ci gaba da dorewar bunkasar tattalin arziki, ya kuma yaba da kwarewar shugabanci da gogewa da ilimi da kuma basirar tsohon firaministan na Kenya.
Mahboub Muaalim ya ce nadin zai taimaka sosai wajen hada karfi da karfe, domin aiwatar da shirin raya ababen more rayuwa na Afrika, yana mai cewa jigo ne cikin ajandar AU ta 2063.
Ya ce a matsayin yankin na wanda ya fi raya ababen more rayuwa, IGAD za ta mara baya ga sabon wakilin wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, yana mai bayyana kudurin kungiyar na cimma burin samar da ababen more rayuwa da ci gaban da nahiyar ke bukata. (Fa'iza Mustapha)