Wata Sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce takunkumin da Amurka ta sanyawa Sudan ya haifar da illa sosai ga tsarin tattalin arziki da siyasa da huldar diflomasiyya na kasar.
A madadinsa da kuma kungiyar IGAD, Amb Mahboub ya taya Gwamnati da al'ummar Sudan murna, bisa irin juriyarsu da fata na gari da dabarun diflomasiyya da suka nuna, duk da dimbin kalubalen da suka fuskanta lokaci mai tsawo na tukunkumin.
Amb Mahboub, ya kuma yabawa Amurka da wannan mataki da ta dauka da zai yi kyakkyawan tasiri ba kadai ga tattalin arzikin Jamhuriyar Sudan ba, har ma da kasashe makwabta da na kungiyar IGAD baki daya. (Fa'iza Mustapha)