Wata sanarwa da kasashe mambobin kungiyar raya yankin na gabashin Afirka ko IGAD a takaice suka fitar ta bayyana cewa, masu ruwa da tsaki ciki hadda kwararru a fannin raya ilimi sun gana, a wani mataki na amincewa da yarjejeniya, da tsarin gudanarwar Djibouti da aka cimma a watan Disambar shekarar bara.
Sanarwar ta ce, ana fatan masana a fannin raya ilimi na yankin za su fitar da wani tsari na hadin gwiwa, wanda kasashen yankin za su yi amfani da shi wajen aiwatar da waccan yarjejeniya ta Djibouti.
Da yake tsokaci game da hakan, ministan ma'aikatar ilimi na kasar Habasha Mohamed Ahmedin, ya ce ilmantar da 'yan gudun hijira, da wadanda suka rasa matsugunnan su, da ma mazauna yankunan dake karbar su, zai taimaka matuka wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin.
Wani rahoto na MDD ya bayyana kasar Uganda, a matsayin ta daya a kasashen yankin dake karbar 'yan gudun hijira mafiya yawa, inda a yanzu take da sama da 'yan gudun hijirar miliyan 1.4, mafi yawan su daga kasashen Sudan ta kudu. (Saminu)