in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara tsaro a Somali yayin da ake dab da fara taron koli na kasashen gabashin Afrika
2016-09-11 12:43:06 cri
Shugaban kasar Somali Hassan Sheikh Mahmud ya fada a jiya Asabar cewa, an girke jami'an tsaro a Mogadishu babban birnin kasar da kewayensa a yayin kasar ke shirye shiryen karbar bakuncin taron koli na kasashen gabashin Afrika a ranar 13 ga wannan wata.

Mahmud ya fada cewa, shugabannin kasashe 8 na mambobin kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD ne zasu halarci taron, wadanda suka hada da Djibouti, Habasha, Kenya, Somaliya, Sudan ta kudu, Sudan, Eritrea da kuma Uganda.

Ana saran taron zai maida hankali ne wajen tattauna batutuwan siyasa da cigaban da aka samu ta fuskar tsaro a kasar Somaliya, da kuma nazartar zaben da ake shirin gudanarwa a kasar tsakanin watan Satumba zuwa Oktoba. Bugu da kari, taron kolin zai maida hankali wajen lalibo hanyoyin warware rikicin Sudan ta kudu.

A yayin zantawarsa da manema labarai a Nairobi shugaba Mahmud, ya bayyana cewa za'a gudanar da taron kolin ne a mako mai zuwa, don haka ya bukaci al'ummar kasar da su hada gwiwa da hukumomin tsaro, domin samun nasarar taron.

Ya kara da cewa, jami'an tsaro za su cigaba da yin sintiri a birnin, ya bukaci jama'ar kasar da su yi hakuri da yanayin da ake ciki kasancewar kasar na shirin karbar bakuncin taro ne na kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China