in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya yabawa kungiyar IGAD bisa rawar da ta taka na farfado da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2017-08-04 10:18:23 cri
Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan harkokin wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya yabawa kokarin kungiyar raya gabashin Afrika IGAD, na farfado da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu tare da lalubo mafita ga rikicin kasar a siyasance.

Jean-pierre Lacroix ya ce yunkurin IGAD na farfado da yarjejeniyar ta 2015, zai bada fatan samun mafita ga rikicin Sudan ta Kudu, yana mai cewa, MDD za ta goyawa kasashen gabashin Afrika baya a kokarinsu na neman dauwamammiyar mafita ga kasar da yaki ya d'aid'aita.

Jami'in ya kuma yi tir da ta'azarar rikici a fadin Sudan ta Kudu, ciki har da kwantar baunar da ake yi wa fararen hula a kan tituna, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane cikin watannin baya, inda ya yi kira ga bangarorin adawa su daina farwa fararen hula tare da kawo karshen ayyukansu nan take.

Har ila yau, ya kara da yin kira ga gwamnatin kasar da sauran kasashe da ke da alhakin taimakawa cimma yarjejeniyar, su gaggauta tura dakarun da za su taimaka wajen dawo da tsaro a babban birnin kasar da sauran sassanta.

Ya ce shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu zai duba yiyuwar baza dakarunsa a kan manyan tituna da wuraren dake da hadari domin kare fararen hula. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China