in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa ta yaba wa ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kare 'yancin bil Adama
2018-11-07 09:23:32 cri
A jiya Talata, tawagar wakilan gwamnatin kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Le Yucheng, ta halarci taron dudduba yadda kasashen duniya ke kare 'yancin bil Adama zagaye na 3, wanda kwamitin kula da harkokin 'yancin bil Adama na MDD ya shirya a birnin Geneva.

A yayin taron, Le Yucheng ya bayar da wani jawabi, inda ya bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kare 'yancin bil Adama, bisa jagorancin kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping.

Mr. Le ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta kafa wani cikakken tsarin kare 'yancin bil adama, da kuma inganta ka'idojin tabbatar da ganin al'ummomin kasar sun samu ikon tafiyar da harkokin kasa da kansu. Ya ce yanzu kasar Sin ta zama kasa wadda ta samu ci gaba sosai cikin sauri wajen kare 'yancin bil Adama.

A yayin da suke dudduba yadda kasar Sin take kare ''yancin bil Adama, wakilin kasashe fiye da 120 ciki har da na Rasha, da Afirka ta kudu, da Pakistan, da Cuba, da kuma Kambodiya, sun bayar da jawabansu daya bayan daya, inda suka yabawa babban ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kare 'yancin bil Adama. Wakilan suna kuma ganin cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci, da kuma tabbatar da ganin al'ummarta ta samu cikakken iko a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma, da kuma raya al'adu yana da muhimmanci matuka, har ma ya bayar da muhimmiyar gudummawa, wajen tabbatar da samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China