in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya sabunta matakan yaki da fasa kaurin danyen mai daga kasar Libya
2018-11-06 14:32:19 cri
A jiya Litinin kwamitin sulhun MDD ya amince da sabunta matakan yaki da laifukan da suka jibinci fasa kaurin albarkatun man fetur daga kasar Libya har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 2020.

Kudurin dokar mai lamba 2441, wanda ya kunshi matakan hana fasa kaurin albarkatun man fetur, ya kunshi batun tsawaita wa'adin dokar wanda kwamitin ya amince da shi karkashin kudurin doka mai lamba 2146 wanda ya zartar a shekarar (2014), dokar ta baiwa kasashe mambobin kwamitin MDD ikon binciken manyan jiragen ruwan dakon danyen mai a kan teku, da daukar duk wasu matakan da suka dace domin dakile fasa kaurin albarkatun mai.

Kudurin dokar dai ya amince cewa dokokin da matakan da aka zartar za'a yi amfani da su ne game da batun da ya shafi yadda ake aikin loda man a jiragen dakon mai ta ruwa, da sufurinsa, ko kuma kwasar albarkatun man fetur din, wanda ya hada da danyen mai da wanda aka riga aka kammala tacewa, wadanda ake fasa kaurinsu ta barauniyar hanya ake ficewa da shi daga kasar ta Libya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China